Jump to content

A.P.J. Abdul Kalam

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
A.P.J. Abdul Kalam
Murya
shugaban ƙasar Indiya

25 ga Yuli, 2002 - 25 ga Yuli, 2007
K. R. Narayanan (en) Fassara - Pratibha Patil (en) Fassara
Rayuwa
Haihuwa Rameswaram taluk (en) Fassara, 15 Oktoba 1931
ƙasa Indiya
Dominion of India (en) Fassara
Harshen uwa Tamil (en) Fassara
Mutuwa Shillong (en) Fassara, 27 ga Yuli, 2015
Yanayin mutuwa Sababi na ainihi (cardiac arrest (en) Fassara)
Ƴan uwa
Abokiyar zama Not married
Karatu
Makaranta St Joseph's College, Tiruchirappalli (en) Fassara
University of Madras (en) Fassara
Oakland University (en) Fassara
Harsuna Tamil (en) Fassara
Talgu
Turanci
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa, military flight engineer (en) Fassara, injiniya, Malami da aerospace engineer (en) Fassara
Muhimman ayyuka Wings of Fire (en) Fassara
Kyaututtuka
Imani
Addini Mabiya Sunnah
Musulunci
Jam'iyar siyasa no value
IMDb nm1527897
abdulkalam.nic.in…
Dr A P J Abdulkalam
Dr.APJ.Abdul Kalam National memorial
A.P.J. Abdul Kalam
A.P.J. Abdul Kalam

(Tamil:அவுல் பகீர் ஜைனுலாப்தீன் அப்துல் கலாம்), 15 ga Oktoban 1931 – 27 ga Yulin 2015) masanin kimiyyar jiragen sararin samaniya ne wanda ya zama shugaban kasar Indiya tsakanin shekarar 2002-2007. An haifeshi kuma ya girma a kauyen Rameswaram, Tamil Nadu kuma ya karanci ilimin kimiyyar kere-kere da ilimin gyara tauraron dan'adam. Ya kuma sha rike mukamai na maigudanarwa a ma'aikatun kimiyya da fasahar kere-kere, mafiya yawanci a Cibiyoyin hukumomin tsaro na kasar Indiya. A sakamakon aikin da yayi a fannin kere-kere ne yasa ake kiran sa da Harsahin Indiya.[1][2][3] Ya kuma bayar da gudunmuwa wajen samar da Nukiliyan Kasar Indiya wato Pokhran-II a 1998, karo na farko tun bayn wanda akayi a 1974.[4]

A.P.J. Abdul Kalam
A.P.J. Abdul Kalam

An zabi Kalam a matsayin shugaban kasar India a 2002 bisa ga goyon bayan jam'iyyar Bharatiya Janata Party mai mulki, da kuma jam'iyyarIndian National Congress mai adawa. Gabadaya anfi sanin sa da Shugaban Al'uma.[5] banyan kammala zango daya kacal na mulkin sa ne sai ya dawo kan rayuwar sa ta baya wato rayuwa irin ta farar hula Rubuce-rubuce da al'amura na harkokin jama'a. Ya samu lambobin yabo da kyaututtuka da dama wadda ta hada da babbar lambar girmamawa ta kasar Indiya wato kyautar Bharat Ratna. Kalam ya rasu ranar 27 ga Yuli 2015 yayin da yake gabatar da jawabi a makarantar Indian Institute of Management Shillong, inda nan take ya fadi kasa, ya rasu yana da shekaru 83.[6] Dubban mutane ne cikin harda jami'n Gwamnatin kasar Indiya suka halarci jana'izar sa da akayi a kayen su na Rameshwaram, inda aka binne shi cikin girmamawa.[7]

  1. Pruthi, R. K. (2005). "Ch. 4. Missile Man of India". President A.P.J. Abdul Kalam. Anmol Publications. pp. 61–76. ISBN 978-81-261-1344-6.
  2. "India's 'Mr. Missile': A man of the people". 30 July 2015. Archived from the original on 25 September 2015. Retrieved 30 July 2015.
  3. "Kalam's unrealised 'Nag' missile dream to become reality next year". 30 July 2015. Archived from the original on 3 January 2017. Retrieved 30 July 2015.
  4. Sen, Amar (2003). "India and the Bomb". In M. V. Ramana; C. Rammanohar Reddy (eds.). Prisoners of the Nuclear Dream. Sangam Books. pp. 167–188. ISBN 978-81-250-2477-4.
  5. Amarnath k Menon (28 July 2015). "Why Abdul Kalam was the 'People's President'". DailyO.in. DailyO. Archived from the original on 13 August 2015. Retrieved 20 August 2015.
  6. Rishi Iyengar (28 July 2015). "India Pays Tribute to 'People's President' A.P.J. Abdul Kalam". Time Inc. Archived from the original on 31 July 2015. Retrieved 20 August 2015.
  7. Neha Singh (30 July 2015). "'People's President' APJ Abdul Kalam Buried with Full State Honours in Rameswaram". International Business Times. IANS. Archived from the original on 19 August 2015. Retrieved 20 August 2015.