Jump to content

Ku kirkiri account domain taimaka ma Hausa Wikipedia. Kirkirar account kyauta ne. Idan kuma neman taimako ku tambaya a nan.

Ayaan Hirsi Ali

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Ayaan Hirsi Ali
member of the House of Representatives of the Netherlands (en) Fassara

30 ga Janairu, 2003 - 16 Mayu 2006
Rayuwa
Haihuwa Mogadishu, 13 Nuwamba, 1969 (55 shekaru)
ƙasa Kingdom of the Netherlands (en) Fassara
Tarayyar Amurka
Ƴan uwa
Mahaifi Hirsi Magan Isse
Abokiyar zama Niall Ferguson (mul) Fassara  (2011 -
Karatu
Makaranta Leiden University (en) Fassara
Harsuna Turanci
Dutch (en) Fassara
Harshen Somaliya
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa, gwagwarmaya, marubin wasannin kwaykwayo, ɗan jarida, scientist (en) Fassara da marubuci
Muhimman ayyuka Submission (en) Fassara
The Caged Virgin (en) Fassara
Infidel (en) Fassara
Heretic: Why Islam Needs a Reformation Now (en) Fassara
Nomad: From Islam to America (en) Fassara
Kyaututtuka
Mamba intellectual dark web (en) Fassara
Imani
Addini Kiristanci
Musulunci
Jam'iyar siyasa Labour Party (en) Fassara
People's Party for Freedom and Democracy (en) Fassara
IMDb nm1748263
ayaanhirsiali.com
Ayaan Xirsi Ali a cikin 2016.
Ayaan Hirsi Ali

Ayaan Hirsi Ali ( an haife ta a ranar 13 ga watan Nuwambar 1969) yar Dutch - Amurka himmar aiki wanda aka haifa a ƙasar Somaliya. An san ta da yin suka game da kaciyar mata a Musulunci. Ita ɗiya ce ga ɗan siyasan Somalia, Xirsi Magan Isse. A shekarar 2005 mujallar Times Magazine ta saka Hirsi a jerin mutane 100 mafiya tasiri a duniya. Xirsi Ali ta zama Ba’amurkiya a shekarar 2013. Ta auri masanin tarihin Burtaniya kuma mai sharhi kan jama'a Niall Ferguson .

Rayuwar farko

[gyara sashe | gyara masomin]

An haifi Xirsi Ali a matsayin Ayaan Xirsi Magan a shekarar 1969 a Mogadishu, Somalia. An saka mahaifinta Xirsi Magan Ciise a kurkuku lokacin da Xirsi Ali ke jaririya. an yi mata kaciya lokacin da take 'yar shekara biyar. [1] Gidan dangin Ali sun yi ƙaura zuwa Saudi Arabiya sannan kuma Habasha. A 1980 suka sake komawa Nairobi, Kenya. Xirsi Ali ta yi karatu a wata Makarantar Sakandiren Mata ta Musulmai.

Rayuwa a cikin Netherlands da Amurka

[gyara sashe | gyara masomin]

A shekarar 1992 Xirsi Ali ta koma Netherlands. Tsakanin 1995 da 2001 ta yi aiki a matsayin mai fassara. Ta fara aiki a matsayin mai bincike na Gidauniyar Wiardi Beckman a 2001. A 2002 ta zama mara addini . Ta zama memba a majalisar Dutch a 2003. Xirsi Ali ce ta rubuta wani gajeren fim wanda Theo Van Gogh ya bada umarni mai suna Submission. An sake shi a cikin 2004. Mohammed Bouyeri ya kashe Van Gogh a ranar 2 ga Nuwamba 2004. Ya bar rubutu a jikin Gogh. Bayanin ya kasance barazanar mutuwa ga Xirsi Ali. A cikin 2006 littafin Xirsi Ali na biyu da aka fassara cikin Turanci, The Caged Virgin: An Emancipation Proclamation for Women and Islam, an buga shi.

A cikin 2013 Xirsi Ali ta zama 'ƴar ƙasar Amurka.

Ayaan Hirsi Ali
Ayaan Hirsi Ali

A shekarar 2014 Jami'ar Brandeis ta yanke shawarar ba wa Xirsi Ali digirin girmamawa. Sannan ba a ba ta digirin ba saboda wani kamfen.

Ra'ayin Siyasa

[gyara sashe | gyara masomin]
Ayaan Hirsi Ali
Ayaan Hirsi Ali
Ayaan Hirsi Ali

Xirsi Ali na goyon bayan Isra’ila a rikicin Isra’ila da Falasdinu .

Gidauniyar AHA

[gyara sashe | gyara masomin]

A 2007 Xirsi Ali ta fara gidauniyar AHA . Gidauniyar ita ce don 'yancin mata.

  1. www.thedailybeast.com