Makaho
Makaho shine mutumin da ya rasa idanunsa ko baya gani da idanunsa guda biyun. Mace kuma ana kiranta da makauniya. Wannan rashin idanun yakasance ciwone irin yanar idanu ko haihuwarsa akayi dashi irinna gado domin bincike ya gano cewa mutum yana iya gadon makanta daga uwa ko daga uba, wandda kwayar cutar na jikin uwa ko uba dan haka, idan ba'a dauki wasu matakai ba a fannin likita, to yayan su na iya daukan wannan cuta, dan haka ta wani fannin ana gadon cutar makanta.
Meke haifarda ita
[gyara sashe | gyara masomin]Abubuwa da dama ne ke haddasa cutar makanta, domin akwai cututtuka da dama da ake kamuwa da su na idanu wadanda idan ba a dauki matakai a kansu ba, sukan iya kaiwa ga makanta. Musali kamar a kasar Nijar, a jihar Damagaram akwai cutar ciwon idon amadari da al'umma ke fama da ita, wadda idan aka dauki matakai tun da wuri, to ba ba za ta kai ga makanta ba, sannan kuma akwai cutuka da su kuma suka danganci tsufa, wandanda idan mutun ya tsufa, to akwai wasu jijiyoyin idanu da suke saki, inda har ake samun cutar yanar idanu, kuma banda haka, akwai ta hanyar jin rauni a idanu, da dai sauran su duk suna iya haddasa makanta.[1][2][3]
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ https://m.dw.com/ha/bayani-kan-cutar-kuturta-da-makanta/a-17634537
- ↑ "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2021-07-26. Retrieved 2021-07-26. More than one of
|archiveurl=
and|archive-url=
specified (help); More than one of|archivedate=
and|archive-date=
specified (help) - ↑ "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2021-07-26. Retrieved 2021-07-26.